China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan

A jiya Litinin ne dai mahukuntan kasar ta China su ka yi Allawadai da yadda kasar Japan din ta girke makamai masu linzami a wani

A jiya Litinin ne dai mahukuntan kasar ta China su ka yi Allawadai da yadda kasar Japan din ta girke makamai masu linzami a wani tsibirinta da yake kusa da yankin Taiwan, tare da bayyana hakan a matsayin kokarin tayar da hargitsi a cikin yankin.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar China Máo Níng ta bayyana cewa: Daukar mataki irin wannan, wanda kuma ya zo bayan furucin Fira Ministar kasar ta Japan Sanae Takaichi,wani yanayi ne mai hatsarin gaske wanda yake da bukatuwa da kasashen yankin su kasance a cikin fadaka, haka nan kuma kungiyoyin kasa da kasa.

Shi kuwa ministan tsaron kasar Japan ya bayyana cewa; Girke makamai masu linzami da kasarsa ta yi a tsibirin Yonagoni dake kusa da Taiwan, zai iya taimakawa wajen ragen yiyuwar kai wa Japan hari.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments