Kasar Chaina ta musanta zargin shugaban kasar Ukraine ga kasar, dangane da tallafawa kasar Rasha da makamai.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar wajen kasar China Lin Jian yana fadar haka a safiyar yau Jumma’a ya kuma kara da cewa, kasar China bata taba daukar bangaren a yakin na Ukraine ba, kuma ra’ayinta shi ne shiga tsakanin don kawo karshen yakin.
Kafin haka dai shugaban kasar Ukraine Volodimir Zelesky ya zargi gwamnatin kasar China da tallafawa kasar Rasha da makamai a yakin da kasarsa take fafatawa da ita. Zelesky ya ce a wannan karon kasar China ta aikawa Rasha makaman Atilari da kuma PorwerGun.
A can baya ma gwamnatin kasar ta Ukraine ta zargi kasar China da tallafawa Rasha da sojojin 155 , sannan tace kasar Rasha na jan China cikin yakin na Ukraine. Gwamnatin kasar China ta musanta dukkan wadan nan zarge-zargen.