Kakakin ma’aikatar harkokin wajen China Lin Jian ne ya jaddada cewa, alakar da take a tsakanin Rasha da China ba ta tasirantuwa da shiga tsakanin wani bangare na uku, sannan kuma ya ce, kokarin da Amurka take yi na haddasa sabani a tsakanin kasashen biyu ba zai yi nasara ba.
A wani taron manema labaru da kakakin ma’aikatar harkokin wajen na China ya gabatar, ya bayar da jawabi akan tambayar da aka yi masa akan maganar da ta fito daga bakin ministan harkokin wajen Amurka Marco Robio cewa; Rasha ta dogara ne China, kuma kasashen biyu za su iya hada kai su yi fada da Amurka.
Li Jian ya kuma ce; Ba tare da la’akari da sauye-sauyen da za su bijiro a fagen siyasar duniya ba, alakar kasashen China da Rasha za ta ci gaba da bunkasa sannu a hankali,don haka kokarin Amruka na haddasa sabani a tsakaninsu ba shi da ma’ana.
A baya kadan shugaban kasar china Xi Jin Ping ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladmir Puitn inda ya bayyana masa cewa, alakar kasashen biyu ba za ta tasirantu ba daga tsoma bakin bangare na kuku.
Ita kuwa fadar mulkin Rasha “Kremlin” ta sanar da cewa, alaka a tsakanin Rasha da China da siyasarsu ta waje suna taimakawa wajen samar da zaman lafiya a duniya, kuma ba a gina alakar tasu domin fada da wani bangare ba.