Chadi: An Kama Tsohon Fira Minista Kuma Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasa

Da safiyar yau Juma’a ne dai jami’an tsaron kasar Chadi su ka kai wani farmaki na   kama tsohon fira minista kuma jagoran ‘yan hamayyar siyasar

Da safiyar yau Juma’a ne dai jami’an tsaron kasar Chadi su ka kai wani farmaki na   kama tsohon fira minista kuma jagoran ‘yan hamayyar siyasar kasar Succès Masra.

Jam’iyyar hamayya da Masra yake jagoranta, ta bayyana abinda jami’an tsaron su ka yi wa jagoran nata da cewa, garkuwa ce.

 Ita kuwa hukumar kasar ba ta fitar da wani bayani akan kamun Masra ba,wanda shi ne ya zo na uku a zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekarar da ta gabata. A yayin wancan zaben dai shugaban ‘yan hamayyar siyasar ya  riya cewa shi ne wanda ya lashe zaben,amma kuma daga baya ya amince da sakamakon da hukumar zabe ta sanar duk da cewa yana cike da kura-kurai kamar yadda ya bayyana.

Bayanin da jam’iyyar adawar ta masu; Sauyi” ta wallafa a shafinta na ‘facebook’ ya kunshi cewa; shugaba Succes Masra an yi garkuwa da shi da karfin bindiga da safiyar yau 16 ga watan Mayu da misalign karfe; 05; 56 daga gidansa da yake kusa da babbar cibiyar jam’iyyar.

A karkashin sanarwar, Shafin jam’iyyar na ‘facebook’ an kuma wallafa hoton bidiyo na shugaban jam’iyyar yana fitowa daga gidansa zagaye da masu dauke da makamai da suke sanye da kakin soja.

Babban mai shigar da kara na kasar ta Chadi Umar Muhammad Kidilayi ya fada wa kamfanin dillancin labarun Faransa cewa lallai an kama Masra.

Masra dan shekaru 41 ya rike mukamin Fira ministan kasar na tsawon watanni 5 gabanin zaben shugaban kasar da aka yi a watan Mayu na 2024.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted