Burtaniya Ta Soki Gwamnatin Netanyahu Kan Hana ‘Yan Majalisarta Biyu Shiga Cikin Isra’ila

Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, David Lammy, ya soki matakin Isra’ila na hana wasu ‘yan majalisar dokokin Birtaniya biyu shiga ƙasar, yana mai cewa matakin bai

Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, David Lammy, ya soki matakin Isra’ila na hana wasu ‘yan majalisar dokokin Birtaniya biyu shiga ƙasar, yana mai cewa matakin bai dace ba kuma abin damuwa ne.

Tsarewa da hana ‘yan Majalisar Wakilan Birtaniya biyu da ke cikin tawagar ‘yan majalisa zuwa Isr’aila shiga cikin ƙasar, abin da ba za a amince da shi ba ne, bai dace ba, kuma babban abin damuwa ne,’ in ji Sakataren Harkokin Waje David Lammy, a cikin wata sanarwa a ranar Asabar.”

Lammy wanda ya bayyana cewa Birtaniya tana tuntuɓar ‘yan majalisar domin ba su goyon baya, kuma ya bayyana wa hukumomin Isra’ila ƙarara cewa “ba haka ake yi wa ‘yan Majalisar Dokokin Birtaniya mu’amala ba.”

“Abin da gwamnatin Birtaniya ta sa a gaba shi ne tabbatar da dawowar tsagaita wuta da tattaunawa domin dakatar da zubar da jini, da ‘yantar da waɗanda aka yi garkuwa da su, da kawo ƙarshen rikicin Gaza,” in ji sanarwar.

Jaridar Times ta Israel ta bayyana sunayen ‘yan majalisar da aka hana shiga a matsayin Abtisam Mohamed da Yuan Yang, tana ambato hukumomi na cewa an hana su shiga ne saboda ƙoƙarin su na “yaɗa kalaman kiyayya kan Isra’ila.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments