Gwamnatin kasar Burkina Faso ta sanar da hana masu harkar shari’a sanya hular farin gashi da ta samo asali daga ‘yan mulkin mallaka.
Shugaban kasar Burkina Faso, Ibrahim Traore ne ya bayar da umarnin haramcin wanda yake a matsayin kokarin raba kasar da al’adun ‘yan mulkin mallaka.
Bugu da kari, an bayyana wannan matakin a matsayin wani yunkuri na tabbatar da al’adun al’ummar Burkina Faso.
Shugaban kasar ta Burkina ya nanata muhimmancin nesantar duk wasu al’adu na turawan mulkin mallaka domin bunkasa al’adun gida.
Burkina Faso ta bi sawun wasu kasashe na nahiyar ta Afirka da su ka yi watsi da wannan al’’adar domin farfado da al’adun cikin gida na Afirka.
Wannan irin hula ta farin gashi da alkalai suke sanya wa tana daga cikin alamun da suke nuni da tasirin kasashen waje a cikin harkar shari’a a nahiyar Afirka.