Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Bakhaei ya bayyana cewa, mashigar ruwa ta Hurmuz zata ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa lokacinda Amurka ta aiwatar da sharuddan kasar guda 7.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasa da kasa, ya nakalto Esmail Bakhaei yana fadar haka ne a safiyar yau litinin, a lokacinda yake jawabi ga kafafen yada labarai kamar yanda ya saba a ko wace ranar likitan.
Dangane da wasikar da mataimakin shugaban kasar Amurka JD Vance ya rubutawa sakataren majalisar tsaro ta kasa kuma, Bakhaei ya ce, ta nuna cewa Amurka bata da wani abunda zata gabatar don kaiwa ga zaman lafiya a yankin. Yace wasikar bata dauke da wani abu sabo, sai dai mu abinda ya kasashen mai muhimanci a wajemmu shi ne gani a kasa. Dole ne a aiwatar da wadannan sharudda guda 7 a kasa.
Don haka a halin yanzu kwallo tana hannun Amurka ta zabi duk abinda take so Iran a shirye take ta bada amsar da ta dace.