Bakaken Fatar Amruka Da Suke Yin Hijira Zuwa Afirka  Suna Karuwa

Ana samun Karin bakaken fatar Amurka da suke baro kasar suna dawo wa nahiyar Afirka domin samun kyakkyawar rayuwa a cikinta. Mafi yawancin bakaken fatar

Ana samun Karin bakaken fatar Amurka da suke baro kasar suna dawo wa nahiyar Afirka domin samun kyakkyawar rayuwa a cikinta.

Mafi yawancin bakaken fatar suna nuna rashin gamsuwarsu da yanayin tattalin arziki da kuma siyasa na Amukra da su ka taka rawa wajen sa su, daukar matakin komawa Afirka da can ne asalin kakanninsu.

Wani dan kasar Amurka da ya rika yawo a tsakanin kasashe mabanbanta na Afirka a karshe ya tare a kasar Kenya, ya bayyana yadda yake jin ya saje a cikin nahiyar Afirka fiye da a can Amurka.

Auston Holleman wanda ya shahara da wallafa sakwanni a You Tube ya kara da cewa; Dukkanin mutane a Afirka sun yi kama da juna, ba  kamar acikin turai, ko yankin Latin ba. “

Holleman ya kuma bayyana cewa yanayin siyasar Amruka a halin yanzu ya sa kasar tana fada da duk duniya baki daya.

Tun a 2019 ne dai kasar Ghana ta kaddamar da wani shiri na jawo hankalin bakaken fata a ko’ina suke a duniya domin samun wurin zama a cikinta.

A shekarar 2024 Ghana din ta ba da izinin zaman ‘yan kasa ga bakaken fata 524,mafi yawancinsu daga kasar Amurka.

Tun bayan da  kamfanonin bakaken fata  na Amurka irin su  Adilah su ka koma Ghana, an sami karuwar bakaken fatar da suke komawa can.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted