Search
Close this search box.

Bagheri Kani: Guguwar Al-Aqsa Ta Sake Farfado Da Batun Falastinu A Duniya

Ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ya ce, farmakin Guguwar Al-Aqsa ya mayar da gwagwarmayar Palasdinu da yankinsu zuwa wani

Ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ya ce, farmakin Guguwar Al-Aqsa ya mayar da gwagwarmayar Palasdinu da yankinsu zuwa wani yunkuri na duniya domin yaki da zaluncin Isra’ila.

Bagheri Kani ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a ranar Talata don tunawa da Ismail Haniyeh, shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Hamas da aka kashe a Tehran babban birnin kasar Iran.

“Tsarin gwagwarmayar Falasdinawa ya yaduwa a duk duniya sakamakon jarumtaka, jajircewa da sadaukarwa. Farmakin Guguwar Al-Aqsa ya canza lissafi da ma’aunai da yawa a duniya. Daya daga cikinsu shi ne rikidewar gwagwarmayar Palasdinawa zuwa gwagwarmaya ta duniya,” in ji Bagheri Kani.

Babban jami’in diflomasiyyar ya ci gaba da cewa, jinin shahidi Haniyyah ya kara karfafa al’ummar Palastinu , yana mai jaddada cewa tsayin daka a duniya wajen nuna kiyayya da zaluncin Isra’ila ya zama wani lamari da ba za a iya musantawa ba.

Haniyeh wanda ya je birnin Tehran domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian tare da wasu shugabannin kungiyar, ya yi shahada a wani hari da aka kai a ranar 31 ga watan Yuli.

Wannan harin ta’addancin ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Tel Aviv take kai hare-haren kisan kare dangi a Gaza.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gargadi Isra’ila kan wani hukunci mai tsanani da ke jiranta, yana mai cewa Iran na kallon daukar fansar jinin Haniyyah a kan Isra’ila a matsayin wani wajibi na addini.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments