Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci jin ra’ayin ba da shawara daga kotun kasa da kasa kan kudurin da aka fitar kan haramtacciyar kasar Isra’ila dangane da batun Falasdinawa
A jiya Alhamis ne Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da shawarar gabatar da bukata ga kotun kasa da kasa kan neman ra’ayin ba da shawara daga kotun game da kudurin wajibtawa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila daukan matakin jin kai ga Falasdinawa.
Kudurin wanda ya yi nuni da mumunan halin da ake ciki na jin kai a Falasdinu, ya yi kira ga gwamnatin mamayar Isra’ila da ta bi ayyukan na shari’a a karkashin dokokin kasa da kasa, kamar yadda kotun kasa da kasa ta bayyana a baya.
Kudurin wanda kasar Norway da akalla kasashe 22 suka gabatar, ya samu goyon bayan kasashe 137, yayin da 12 suka nuna kin amincewa da shi, sannan kasashe 22 suka ki kada kuri’a.
Kafin kada kuri’ar, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Norway Andreas Kravik ya ce: “Sun fahimci cewa kasashe na iya daukar matsayi daban-daban dangane da dalilan da suka haifar da wannan mummunan mafarki mai ban tsoro, amma abin da ba za a iya samun sabani a kansa ba shi ne wajibcin bayar da taimako ga wadanda suka fi bukata.