Babban Sakataren Hizbullahi Ya Ce: Juyayin Arba’in Yana Da Alaka Da Juyayin Kisan Gilla Ga Fouad Shukr

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa: Juyayin ranar Arba’in na gwagwarmayar Imam Husaini {a.s} yana da alaka da kisan gillar da

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa: Juyayin ranar Arba’in na gwagwarmayar Imam Husaini {a.s} yana da alaka da kisan gillar da aka yi wa Fouad Shukr

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya tabbatar da cewa: Tunawa da ranar Arba’in ta Imam Husaini {a.s}, alama ce ta sadaukarwa, kin zalunci, da kuma mika wuya, gami da tabbatar da juyin juya hali har zuwa tashin kiyama.

Sayyid Nasrallah ya jaddada cewa: Miliyoyin masu ziyara daga ciki da wajen kasar Iraki suna tunkarar Karbala ne domin lamari ne da ake tunatar da su gwagwarmayar Imam Husaini {a.s} a duk shekara, kuma ya mika godiya ga gwamnatin Iraki da kuma al’ummar kasar masu karimci kan abin da suke karbar bakwanci da ciyar da masu ziyara, yana jinjinawa Falasdinawa har daga birnin Qudus da suka ziyarci taron Arba’in wanda ke nuni da kasancewar waki’ar Karbala a cikin lamarin Falastinu.

A cikin jawabinsa, Sayyid Nasrallah ya kuma yi ta’aziyya ga al’ummar Lebanon kan rasuwar tsohon fira ministan kasar Salim al-Hoss, wanda ya kasance wata alama ta gwagwarmaya da rikon amana da kishin kasa, yana mai cewa Fira Minista al-Hoss ginshiki ne ga gwagwarmaya har zuwa karshen rayuwarsa, kuma suna jin wannan zafin rashi da fatan Allah ya jikansa da rahamarsa.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments