Babban Muftin Oman Ya Yi Suka Kan Taron Kungiyar Larabawa Saboda Rashin Bai Wa Gaza Muhimmanci

Babban Mufti na kasar Oman ya bayyana cewa: Matakin taron kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ya fi kankara sanyi da rashin muhimmanci Babban Mufti na

Babban Mufti na kasar Oman ya bayyana cewa: Matakin taron kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ya fi kankara sanyi da rashin muhimmanci

Babban Mufti na masarautar Oman, Sheikh Ahmed bin Hamad Al-Khalili, ya jaddada yabonsa ga fitaccen matsayi na kasar Yemen da kuma matsin lamba da dakarun kasar Yemen suke yi na kai kayan agaji a zirin Gaza. A gefe guda kuma, ya nuna rashin jin dadinsa da raunin kudirin taron kasashen Larabawa kan daukan matakan matsin lamba kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da take aiwatar da kashe-kashen gilla kan al’ummar Falasdinu.

A wani rubutu da ya yi a dandalin X, Al-Khalili ya bayyana godiyarsa ga jaruman kasar Yemen da kuma kasashen da suka bayar da gudumawa wajen matsin lamba don saukaka shigar da kayan agaji Gaza, yana mai cewa, “Ya gode wa Allah da shigar da wasu agajin da aka yi a Gaza,” yana mai jaddada bukatar ci gaba da daukan matakan matsin lamba na kasa da kasa wajen bude mashigar agaji gaba daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted