Babban mai shiga tsakani na kungiyar gwagwarmayar falasdinawa ta Hamas Khalil Al-Hayya ya isa Masar, inda ya jagoranci tawagar da ake sa ran za ta fara tattaunawa wacce ba ta kai tsaye ba da Isra’ila, a cewar kungiyar.
Hamas ta ce za a fara tattaunawar ce kan “hanyoyin tsagaita bude wuta, da janye sojojin mamaya, da musayar fursunoni.”
yau Litinin ne aka tsara tawagar Isra’ila za ta isa wurin, kamar yadda ofishin Benjamin Netanyahu ya bayyana, a wani bangare na tattaunawar.
Su ma wakilan Amurka, Masar da kuma Qatar zasu halarci tattaunawar a matsayinsu na masu shiga tsakani.
A cewar majiyoyin diflomasiyya, tattaunawar tsakanin Isra’ila da Falasdinawa za ta gudana ne a birnin Sharm el-Sheikh.
Ana sa ran tattaunawar za ta mai da hankali kan lokaci da cikakkun bayanai don ba da damar sakin ‘yan Isra’ila da aka yi garkuwa da su.
Tattaunawar za ta gudana ne tsakanin Isra’ila a bangare guda da kuma ‘yan Hamas a daya bangaren amma ba keke-da-keke ba, kuma za’a nisanta kafafen yada labarai daga tattaunawar.
Hamas dai ta dage kan bukatar dakatar da dukkan ayyukan soji da kuma na Isra’ila.
Bayanai sun ce sojojin Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare a birnin Gaza har zuwa jajibirin tattaunawar, inda suka kashe gomman mutane kamar yadda hukumar tsaron farar hula ta yankin ta sanar.