Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin musulunci (IRGC Navy) na kasar Iran yace kasashen duniya zasu yi mamaki idan an kaddamar da wani jirgin yakin da suka kera.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Alireza Tangsiri ya na fadar haka a gefen bikin baje kolin jiragen sama na kasa da kasa wanda ke guna a halin yanzu a tsibirin Kish na kudancin kasar a jiya Laraba.
Rear Admiral Alireza Tangsiri ya kara da cewa jirgin yakin wanda ake sarrafa shi daga nesa, ya na daga cikin ayyukan ci gaba mai muhimmanci wanda sojojin ruwa na kasar suka yi.
Tansiri, har’ila yau ya kara da cewa, masana da kwararru na cikin sojojin ruwa na kasar ne suka kirkiru suka kuma samar da irin wannan jirgin yakin wanda ake sarrafa shi daga nesa.
Jami’in sojan ya kammala da cewa sojojin ruwa da sojojin sama har iyala yau da sojojin kasa na JMI suna iya amfani da wannan jirgin yakin a duk wani aikin da ake bukatar irinsa.
Yace hadin kai tsakanin bangarori daban daban na sojojin JMI a samar da irin wannan ci gaban, zai taimakawa bangaren tsaron kasar daban-daban sosai.
A cikin watan Jenerun wannan shekara ma, hadin giwar sojojin da kuma dakarun IRGC sun kaddamar da wasu kayakin aikin soje wadanda suka hada da jiragen sama wadanda ake sarrafasu daga nesa sabbi.