Babban Kwamandan Sojojin Kasar Iran Yace Hare Hare Na Gaba Kan HKI Zai Kasnace Kan Tattalin Arzikin kasar Ne

Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran ya yace a hare haren sojojin kasar zasu kai kan HKI nan gaba zai maida hankali ne kan lalata

Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran ya yace a hare haren sojojin kasar zasu kai kan HKI nan gaba zai maida hankali ne kan lalata tattalin arzikin kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Manjo Janar Mohammad Hussain Bakiri yana fadar haka a wata hira da aka yi da shi a wata tashar Talabijin na kasar. Ya kuma kara da cewa a hare haren jiya Talata sun maida hankali ne wajen lalata cibioyoyin tsaro na HKI kuma kashi 90% na makamai masu linzamin da suka cilla sun sami bararsu kamar yadda aka tsara.

Manjo Janar Bakiri ya ce a hare haren daren Talata sun lalata cibiyar tsaro na HKI na hukumar liken irin HKI wato Mossad, da sansanonin sojojin Nevatim da Hatzerim,. Har’ila yau sun lalata na’urorin Rada da tankunan yakin HKI a wurare da dama.

Janar Bakiri ya bayyana cewa Iran zata iya wargaza cibiyoyin tattalin arzikin HKI a hare haren na jiya amma ta zami cibiyoyin tsaron kasar kadai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments