Babban Kwamandan Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci Ya Yi Bayani A Gaban Majalisar Shawarar Musulunci

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya gabatar da jawabi a gaban Majalisar shawarar Musulunci ta kasar Kakakin kwamitin kula da

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya gabatar da jawabi a gaban Majalisar shawarar Musulunci ta kasar

Kakakin kwamitin kula da tsaro da harkokin waje na Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Ibrahim Reza’e ya bayyana cewa: Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Manjo Janar Hussein Salami ya gabatar da nazari kan halin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki a yayin zaman Majalisar Shawarar Musulunci na musamman a safiyar yau Talata. Reza’e ya wallafa a shafin sada zumunta na dandalin “X” cewa: Bayan nazarin halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya, babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Janar Salami ya kara da jaddada cewa: Karfin Iran bai ragu ba, kuma Iran tana sane da dukkanin muhimman muradun makiya tarayuwa, kuma kawar da tsagerancin yahudawan sahayoniyya yana daga cikin ajandar dakarunsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments