Jagoran juyin juya halin musulunci Aya. Sayyid Mujtaba Khaminaei, ya bayyana cewa, ilmi da halaye masu kyau zasu zama, garkuwan karfe ga Iraniyawa daga makiyansu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jagoran yana fadar haka, a sakon da ya aikawa daliban makarntu da Jami’o’in kasar a dai dai lokacinda ake fara sabon shekarar karatu a yau Talata.
Jagoran ya kara da cewa, a dai dai lokacinda zalunci da karfi suka zama su ne suka mamaye mafi yawan duniya, ilmi idan ya hadu da tsoron All..suna zasu zama garkuwan karfe ga Iraniyawa kuma sune takobi mai kaifi wanda zai yanke hannun makiya daga cutar da mutane.
Jagoran yayi kira ga daliban jami’a da kananan makarantu su yi amfani da karantunsu don gina kwarewarsu a fannin ilmi masu yawa, su kuma karfafa dangantaka da iyaye da yan’uwansu dalibai da na kasa don samun ci gaban kasa.
Yace, ya zama wajibi a kan ko wani dalibi ya gabatar da wata gudumawa don gina kasa nan gaba. Su karfafa kansu a ilmin fasahar zamani da technologiya don kawo ci gaban kasar Iran. Daga karshe jagoran ya yi kira ga daliban makarantu kada su manta da yanuwansu shahidai wadanda Amurka ta kashe a ranar 28 ga watan fabrayrun da ya gabata . Musamman yan makarantar shajarat Attayyiba na garin Minab. Inda kimani 160 daga cikinsu suka yi shahada.