AU Ta Sake Tabbatar da Matsayinta Kan Gyaran Kwamitin Tsaro na MDD

Tripoli ta karbi bakuncin taron a ranakun 10 da 11 ga Oktoba, wanda aka sadaukar domin duba matsayin nahiyar a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin

An gudanar da taron ministoci na 14 na Kwamitin Shugabannin Kasashe da Gwamnati na Tarayyar Afirka da ake kira (C10) a babban birnin Tripoli na Libya, tare da halartar wakilai daga kasashe mambobi, a matsayin wani bangare na kokarin hade matsayin Afirka da kuma karfafa tasirin diflomasiyya na nahiyar a cikin tsarin Majalisar Dinkin Duniya.

Tripoli ta karbi bakuncin taron a ranakun 10 da 11 ga Oktoba, wanda aka sadaukar domin duba matsayin nahiyar a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da kuma fafutukar samar da wakilci mai adalci na nahiyar a kwamitin.

A wannan karon, Libya ta sake jaddada kudirinta na goyon bayan matsayin Afirka baki daya, wanda ke neman kujeru biyu na dindindin a Kwamitin Tsaron, gami da ‘yancin kin amincewa, da kuma karin kujeru biyu wadanda ba na dindindin ba.

Ministan Harkokin Wajen Libiya, Taher Al-Baour ya bayyana cewa dole ne cibiyoyin kasa da kasa su nuna “gaskiya a duniyar yau, ba zamanin da ya gabata ba.”

Kwamitin Tarayyar Afirka na Goma ne ke da alhakin daidaita matsayin nahiyar a tattaunawar gwamnatoci kan gyaran kwamitin Tsaro.

Ƙungiyar ya kunshi kasashe goma: Libya, Aljeriya, Kongo, Equatorial Guinea, Kenya, Namibia, Senegal, Sierra Leone, Uganda, da Zambia. Sierra Leone ce ke shirya taron.

Taron na Tripoli ya zo ne a daidai lokacin da Libya ke neman kujera a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, a cewar majiyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted