AU ta sake watsi da ikirarin Trump cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya

Shugaban Kwamitin Tarayyar Afirka ya yi watsi da zargin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa ana wa Kiristoci kisan kare dangi a arewacin

Shugaban Kwamitin Tarayyar Afirka ya yi watsi da zargin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa ana wa Kiristoci kisan kare dangi a arewacin Najeriya.

Da yake jawabi a wani taron Majalisar Dinkin Duniya a New York, ya ce irin wadannan kalamai kan iya gurbata matsalolin tsaro mai sarkakiya.

Da yake magana tare da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres a ranar Alhamis, Mahmoud Ali Youssouf ya jaddada cewa Tarayyar Afirka ta riga ta fayyace matsayinta kuma ta yi kira da a yi taka tsantsan a cikin harshen da ake amfani da shi wajen bayyana rikice-rikicen da ke faruwa a nahiyar.

“Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya,” in ji Youssouf. “Mun fitar da wata sanarwa a fili da ke nuna cewa abin da ke faruwa a arewacin Najeriya ba shi da alaka da ta’addancin da muke gani a Sudan ko a wasu sassan gabashin DRC.”

Musulmai da Kiristoci, dukkansu abin ya shafa inji shi…

Ya kara da cewa tashin hankalin da ake yi a arewacin Najeriya, wanda galibi kungiyoyin ta’addanci na Boko Haram da ISIS a Yammacin Afirka ke haifarwa, ya shafi Musulmai da Kiristoci.

“Ina ganin lamarin arewacin Najeriya ya kamata mu yi taka tsantsan kafin mu yi irin wadannan kalamai,” in ji Youssouf.

 “Musulmai ne suka fara shan wahala a hannun Boko Haram, ba Kiristoci ba, kuma ina faɗin haka ne bisa bayanai da muke dasu.”

A kwanan baya ne shugaba Trump na Amurka ya bayyana cewa zai doki matakin soji a Najeriya bisa zargin cewa gwamnatin kasar na kauda kai a game da kisan da y ace ana wa Kiristoci a kasar batun da Najeriya ta musanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted