Mataimakin Shugaban Kasa na Farko na Iran ya ce, “Iran tana da alaƙar haɗin gwiwa na musamman da al’adu da dukkan ƙasashe membobin Ƙungiyar Haɗin Kan Shanghai (SCO), kuma abin farin ciki, ƙasar Iran ta shiga ƙungiyar SCO a hukumance cikin shekaru biyu da suka gabata.”
Da yake jawabi a Filin Jirgin Sama na Mehr-abad kafin ya tashi zuwa Rasha don halartar taron kolin kungiyar Shaanghai ta SCO, Mataimakin Shugaban Kasa na Farko Mohammad Reza Aref ya ce, “Ƙungiyar SCO ƙungiya ce mai tasowa amma mai ƙarfi da cikakken iko. Jimillar yawan al’ummar ƙasashe goma wadanda suke mambobi a kungiyar sun kai kimanin biliyan 3.4.”
Ya ƙara da cewa, “Iran tana da alaƙar haɗin gwiwa tsakanin na musamman da al’adu da dukkan ƙasashe membobin kungiyar, kuma abin farin ciki, Iran ta shiga ƙungiyar ta SCO a hukumance cikin shekaru biyu da suka gabata. Duk da cewa tsarin zama memba a kungiyar ya dauki lokaci mai tsayi sosai, kuma kafin shigar Iran cikin kungiyar tana da kyakkyawar haɗin gwiwa da wannan ƙungiyar.”