Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Ƙarfin kariya da makamai masu linzami na Iran ne suka tilasta wa abokan gaba neman tsagaita wuta
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa: Karfin kariya da makamai masu linzami na Iran, sune suka tilasta wa makiya neman tsagaita wuta.
Wannan dai ya zo ne a cikin wata sanarwa da ministan harkokin wajen kasar ta Iran Abbas Araqchi ya fitar a lokacin da ya ziyarci gidan tsohon kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci nak are tsaron sararin samaniyar Iran, Manjo Janar Amir Ali Hajizadeh, inda ya mika ta’aziyyarsa da taya shi murnar rabauta da shahada tare da nuna girmamawa ga daukakarsa.
Araqchi ya yi ishara da irin kokarin da shahidi Manjo Janar Amir Ali Hajizadeh ya yi a kan turbar daukakar Jamhuriyar Musulunci ta Iran yana mai cewa: Karfin makamai masu linzami na Iran da karfin kariya daga irin kokarin kasa da na addini da kuma na wannan shahidi mai girma da sahabbansa ne, kuma wadannan kokari ba za su taba bacewa a tarihin al’ummar Iran ba.