Araqchi: Wajibi Ne Kasashen Yankin Gabas Ta Tsakiya Su Hada Kai Domin Dakile Isra’ila

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya ce cin zarafin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi, na da matukar hadari ga zaman lafiya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya ce cin zarafin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi, na da matukar hadari ga zaman lafiya da tsaro a yankin da ma duniya baki daya.

Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da takwaransa na Kuwait Abdullah Ali al-Yahya a birnin New York, inda jami’in na Iran yake halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79.

“Ya kamata kasashen yankin su hada kai da juna domin dakile munanan ayyukan wannan gwamnati,” in ji Araghchi.

“Saboda haka, Jamhuriyar Musulunci ta mayar da hankali matuka kan yin shawarwari da kasashen da ke a kudancin Tekun Fasha,” in ji shi.

Kalaman Araghchi sun zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da yakin kisan kiyashi a kan al’ummar zirin Gaza da kuma kara kai hare-hare a yankin yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye , da kuma yadda take zafafa hare-haren wuce gona da iri kan kasar Labanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments