Araqchi: Kare iyakokin siyasa na kasashen yankin jan layi ne ga Iran

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce kare iyakokin siyasa da kuma ikon kasa na kasashen yankin shi ne jan layi na Tehran kuma

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce kare iyakokin siyasa da kuma ikon kasa na kasashen yankin shi ne jan layi na Tehran kuma babban abin damuwa.

Araghchi ya bayyana hakan ne a wata makala da aka wallafa  a jaridar Al-Nahar ta kasar Lebanon a ranar wannan Talata.

Ya jaddada cewa kasancewar Iran a Siriya ya kasance bisa bukatar gwamnatin kasar da nufin yakar kungiyar ta’addanci ta Daesh.

Araghchi ya ce, kasancewar a Syria ba kamar kasancewar Amurka a kasar ba ne, domin kuwa Amurka ta yi gaban kanta ne wajen shiga Syria ba tare da izinin kowa ba, tare da mamaye wasu yankuna na kasar.

Haka nan kuma ya jaddada aniyar kasar Iran na goyon bayan dukkanin dakarun musulmi da na larabawa wadanda ke da aniyar ganin sun tinkari mamayar da  gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi a cikin kasashen yankin.

Ya jaddada cewa gwagwarmaya wajen tunkarar manufofin Haramtacciyar Kasar Isra’ila a yankin, shi ne kadai mafta wajen kare ‘yanci da kuma tsaron yankin baki daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments