Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya ce ya karbi wata wasika daga shugaban kasar Amurka Donald Trump ta hannun manzon kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Araghchi ya bayyana cewa, na karbi bakuncin Anwar Gargash mai baiwa shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa shawara kan harkokin diflomasiyya. Baya ga tattaunawa kan huldar dake tsakanin kasashen biyu da kuma batutuwan yankin, na samu wasikar shugaban kasar Amurka.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa, tuni aka mika wannan wasika ga jagoran juyin juya hali domin yin nazari a kanta, da kuma daukar matakin da ya dace dangane da wasikar.
Wasu bayani na cewa wasikar dai tana kunshe ne da wani sako da ke neman Iran da ta shiga tattaunawa kai tsaye tare da Amurka dangane da batun shirinta na nukiliya.
A baya dai Trump da kansa ya yi ikirari a wata hira da Fox Business cewa ya aike da wasika zuwa ga jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.
Jami’ai daban-daban na Iran ciki har da Araghchi, sun yi watsi da ikirarin na Trump.
Baya ga haka kuma Iran ta sha nanata cewa ba za ta shiga duk wata tattaunawa da amurka a karkashin matsin lamba ko barazana ba.