Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Amurkawa sun yi kuskure idan suna tunanin cewa hari kan cibiyoyin makamashin nukiliya zai canza matsayin Iran ko kuma ya sa ta ja da baya
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Dole ne a fara wani sabon mataki na dangantaka tsakanin Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA saboda gaba daya sabbin al’amura sun bullo. Dokokin majalisar Shawarar Musulunci da yanayin filin sun canza, kuma an kai hari da bama-bamai da kuma lalata cibiyoyin makamashin nukiliya da yawa.
Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana cewa, Amurkawa sun yi kuskure idan har suna tunanin kai hari kan cibiyoyin makamashin nukiliya zai sauya matsayin Iran ko kuma ya sa ta ja da baya.
A cikin shirin “Tehran, Iran, duniya” da aka watsa a tashar talabijin ta Tehran a yammacin jiya Laraba, yayin da yake amsa tambaya kan sabuwar hanyar tunkarar hukumar ta IAEA, Araqchi ya bayyana cewa: Majalisar shawarar Musulunci ta zartas da wata doka mai matukar muhimmanci, inda ta mai da hadin gwiwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da hukumar zuwa hukunce-hukuncen kwamitin koli na tsaron kasar, wanda hakan na nufin duk wani hadin gwiwa da hukumar daga yanzu dole ne a gudanar da shi ta hanyar majalisar koli ta tsaron kasar.