Araqchi: Har yanzu Iran ba ta mayar da amsa ga wasikar Trump kan tattaunawar nukiliya ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya sanar da cewa har yanzu Iran ba ta mayar da martani kan wasikar da shugaban Amurka Donald

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya sanar da cewa har yanzu Iran ba ta mayar da martani kan wasikar da shugaban Amurka Donald Trump ya aike kan shirin nukiliyar Iran ba. Sai dai ya ce ana shirin mayar da amsa kuma za a mika ta hanyoyin da suka dace nan ba da jimawa ba.

Da yake magana a wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da ministan harkokin wajen Armeniya Ararat Mirzoyan a Yerevan, Araghchi ya nanata cewa Iran ba za ta shiga tattaunawa kai tsaye da Amurka ba a karkashin yanayin matsin lamba da  barazanar soji, da kuma kakaba takunkumi.

Sai dai kuma ya tabbatar da cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai uku, tare da tabbatar da aniyar Iran ta fuskar diflomasiyya.

Wasikar wadda Trump ya sanar da aikewa da ita a ranar 7 ga Maris, an aike da ita ne zuwa ga jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatullah Sayyed Ali Khamenei,  a daidai lokacin da gwamnatin Amurka ke ci gaba da aiwatar da matakai na matsin lamba a  kan Iran, a daya bangaren kuma take nuna sha’awar yin shawarwari tare da kasar ta Iran.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran Esmaeil Baqaei ya fayyace cewa Tehran ba ta da wani shiri na bayyana wasikar a bainar jama’a, yana mai cewa ba lallai bane jita-jitar da kafafen yada labarai suka yada a game da wasikar ya zama gaskiya.

Za a yi martanin ne game da wannan wasiku ta hanyoyin diflomasiyya bayan yin cikakken nazari a kai, in ji shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments