Araqchi: Dole ne al’ummomin yankin su hada kai domin  dakatar da hare-haren Isra’ila a Syria

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi tsokaci game da hadarin da ke tatatre da hare-haren da Isra’ila take kaddamarwa a kan kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi tsokaci game da hadarin da ke tatatre da hare-haren da Isra’ila take kaddamarwa a kan kasar Syria, yana mai jaddada wajabcin hadin kai tsakanin kasashen yankin domin dakile munanan munanan manufofin Isra’ila  akan Syria.

Araghchi ya ce gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi yunkurin ruguza kusan duk wani abin da ya shafi tsaro da kayan morev rayuwa na fararen hula a kasar ta Siriya “kuma ta mamaye wasu yankunan kasar Siriya wanda ya saba wa yarjejeniyar kasa da kasa ta 1974 da kuma kudurin kwamitin sulhu na MDD mai lamba 350.”

Ya soki Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kasa yin wani katabus, yana mai cewa, “Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya – wanda ke da alhakin dakatar da duk wani aikin cin zarafi da sabawa dokokin kasa da kasa, ya koma kwamitin sanya ido a karkashin kulawar Amurka.”

Araghchi ya jaddada cewa, makwaftan kasar Syria, da  larabawa da musulmi, da ma duk wata kasa mai mai ‘yancin siyasa mamba a MDD dake bin doka da oda, da muhimman ka’idojin yarjejeniyar MDD da dokokin kasa da kasa, ba za su iya nuna halin ko in kula ba.

Rundunar sojin Isra’ila ta yi ikirarin samun gagarumar nasara wajen wargaza kayan yaki  sojojin Syria a wani gagarumin hari ta sama, wanda aka bayyana a matsayin daya daga cikin mafi girma da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta taba kaiwa a tarihinta.

A cewar kafofin yada labaran Isra’ila da suka hada da Walla da Maariv, farmakin da aka yi wa lakabi da Operation Bashan Arrow, ya shafi manyan makamai na Syria, kuma an kaddamar das hi ne a  cikin sa’o’i 48. Alkalumma sun nuna cewa kashi 70-80% na kayayyakin aikin soja na sojojin Siriya sun lalace.

Shafin yada labarai na Walla ya bayar da rahoton cewa, sake gina karfin rundunar sojojin Syria zai bukaci “daruruwan biliyoyin daloli” kuma zai iya daukar gwamman shekaru masu zuwa.

Rahoton ya yi nuni da cewa sojojin kasar Syria da a da ake daukar su a matsayin wani gishiki na karfin sojin kasashen larabawa, amma sakamakon makircin da aka ta kitsa musu tsawon shekaru , hakan yasa sun yi rauni, wanda hakan ne ma yasa a lokacin farmakin ‘yan ta’adda wanda ya fara daga shekarar 2011, kasashen Rasha da Iran suka taimaka ma kasar wajen tunkarar kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka shiga kasar daga kasashen duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments