Arakchi: Sakamakon zaben Amurka ba zai shafi manufofin Iran ba

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce sakamakon zaben Amurka ba zai shafi manufofin Tehran ba, yana mai gargadin “makiya Iran” da kada su

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce sakamakon zaben Amurka ba zai shafi manufofin Tehran ba, yana mai gargadin “makiya Iran” da kada su kuskura su gwada Iran.

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar  da cewa, kasarsa ba kallon zaben Amurka da wata kima, balantana sakamakon zaben ya yi wani tasiri a akan manufofin Tehran.

Kalaman na Araqchi sun zo ne a matsayin Karin haske kan ko sakamakon zaben shugaban kasar Amurka da ake gudanarwa a wannan Talata zai iya yin tasiri kan manufofin Iran, musamman a lokacin da ake Magana kan yiwuwar mayar da martanin Iran kan harin haramtacciyar kasar Isra’ila.

Ya kara da cewa: “Ko shakka babu za mu mayar da martani kan gwamnatin ‘yan sahyuniya ta hanyar da ta dace, to amma yanayi da ingancin wannan martanin ya dogara ne da shawarar Jamhuriyar Musulunci da kuma yanayin da ake ciki,” yana mai bayanin cewa kowa ya sani kuma ya shaida hakan.

Ministan harkokin wajen Iran ya ce: “Muna gaya wa makiya  cewa kada su gwada karfinmu, kuma za su ga sakamakon idan sun yi hakan,” ya kara da cewa: “Ba za mu yi watsi da ka’idojin da muke da su ba, kuma ba za mu yi shawarwari da kowa a  kansu ba.”

Haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai hari ta sama kan Iran, kuma ta sanar da cewa za ta kai hari kan wuraren da sojoji suke ” amma Tehran ta tabbatar da cewa ta yi nasarar tinkarar wadannan ayyuka na ta’addanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments