Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araghchi ya jaddada cewa, babban burin kasarsa shi ne tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin baki daya.
Araghchi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da babban hafsan hafsoshin sojin kasar Pakistan da kai ziyara a birnin Tehran a wannan Laraba.
Bangarorin biyu sun tattauna kan batutuwa da suka kyakkayawar alaka da hadin gwiwa na tsaro da ke tsakanin kasashensu.
Baya ga haka kuma sun yi dubi kan sauran batutuwa da suka shafi halin da ake ciki a yankin, da kuma yin shawara kan ayyukan hadin gwiwa a tsakaninsu.