Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi watsi da labarin da ministan harkokin wajen kasar Jamus ya watsa dangane da shirin Nukliyar kasarsa ya kuma kara da cewa labarin jabu ne.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X . Ya kuma yi watsi da zancen ministan harkokin wajen kasar Jamus wanda yake cewa, jinginar da aiki tare da hukumar makamashin nukliya ta duniya wato IAEA wanda JMI ta yi, ya na nuna cewa ba wanda zai bincika ayyukanta na makamashin nukliya ba, kuma ta rufe kofar tattaunawa Kenan.
Aragchi ya bayyana cewa wannan ba haka bane, saboda shirin nukliyar kasar Iran a halin yanzu ya na karkashin majalisar koli ta tsaron kasar Iran ne, don haka ita ce zata fayyece yadda huldar shirin zai kasance tare da hukumar IAEA. Sannan Iran bata fice daga yarjeniyar NPT ba.
Kasar Jamus dai tana goyon bayan hare=hare da HKI da AMurka suka kaiwa JMI a yakin kwanaki 12, daganĀ cikin harda hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliyar kasar. Ya ce aiki ne da bai dace ba wacce JKI ta yi madadin kasashen yamma.