Ministan harkokin wajen kasar Iran Abass Aragchi ya bayyana cewa, Iran ta karbi jawabin Amurka dangane da shawarar bude mashigar ruwa ta Hurmuz a cikin mako guda ko kwanaki 7 wanda JMI tagabatar a lokacin babban taron shuwagabannin kasashen duniya a MDD kuma nan gaba za’a tattauna a kanta a yau a nan birnin Tehran.
Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto majiyar ma’aikatar harkokin wajen kasar na cewa, Abbas Aragchi da tawagarsa sun gana da masu shiga tsakani a birnin doha na kasar Qatar inda suka karbi jawabin Amurka kan shawarar bude mashigar ruwa ta Hurmuz a cikin kwanaki 7.
Labarin ya kara da cewa a cikin shawarar dai Iran ta gabatar da sharuddanta na bude mashigar wadanda, Idan Amurka ta amince za’a bude mashigar a cikin kwanaki 7, tare da cika sharuddanta.