Aragchi Ya Bayyan Kokarin Ma’aikatarsa Na Bukatun Iran A Shirinta Na Makamashin Nukliya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyanawa kwamitin al-amuran harkokin waje na majalisar dokokin kasar iran kokarin da ma’aikatarsa take na kare muradun

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyanawa kwamitin al-amuran harkokin waje na majalisar dokokin kasar iran kokarin da ma’aikatarsa take na kare muradun JMI na amfana da fasahar makamashin nukliya.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa an gudanar da taron ne, a ma’aikatar harkokin wajen kasar a jiya Lahadi. Kuma ministan ya bayyana wa kwamitin dalla dalla kan irin sabbin kokarin diblomasiyya wanda ma’aikatar take yi don ganin ta kare halattaccen shirin makamashin nukliya na kasar Iran.

Ministan ya bayyanawa kwamintin, irin ayyukan da ma’aikatarsa ta yi a shekarar da ta gabata a bangaren makamashin Nukliya, kara kyautata dangantaka da kasashe makobta, da ci gaba da karfafa zumunci da manya-manyan kungiyoyi da kasa shen duniya wadanda suka hada da kasashen Kudu-masu kudu, da kungiyar BRICS da Shanghai da sauransu wajen tallafawa tattalinarzikin diblomasiyya na kasar Iran.

Har’ila yau ya yi masu karin bayani kan ziyarar  aiki wanda shugaba Masoud Pezeshkiya yayi a birnin NewYork inda ya halarci taron babban zauren MDD karo 80. Da kuma tarurrukan gefen taron da shi da shugaban kasa suka gudanar. Daga ciki har da kokarin tunkude shirin kasashen turai guda uku na maida takunkuman tattalin arzikin MDD kan JMI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments