Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya mayarwa shugaban kasar Amurka Donal Trump martani dangane da fadinsa, kan cewa zai kwace iko da mashigar ruwa ta Hurmuz ya kuma karbi haraji na kasha 20% na dukkan kayakin da jiragen ruwa masu wucewa ta mashigar suke dauke da su.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Litinin, ya kuma kara da cewa mashigar ruwa ta Hurmuz bangare ne na kasar Iran kuma zata ci gaba da zama karkashin kula na kasar har abada.
Sannan ya kammala da cewa, gaskiya ne duk wanda yake iko da mashigar yakamata ya karbi kudaden daga jiragen da suke son wucewa ta cikinta, amma kasha 20% yayi yawa, Iran zata yi adalci, inji ministan.