Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya ce: Miliyoyin ‘yan Sudan da Falasdinawa na cikin hadarin fuskantar mutuwa daga cututtuka
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa: Miliyoyin ‘yan Sudan da Falasdinawa a Zirin Gaza na cikin hadarin fuskantar mutuwa kuma ba kawai daga hare-haren bama-bamai ba har ma da cututtukan da suke kunno kai sakamakon hare-haren da ake kai wa kan cibiyoyin lafiya.
A wani sakon faifan bidiyo da ya gabatar a yayin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Guterres ya kara da cewa: Duniya tana cikin matsaloli, daga matsalar canjin yanayi zuwa ga karuwar masifar talauci da rashin daidaito da yawaitar tashe-tashen hankula, yayin da rikici ya kunno kai, kiwon lafiya na fuskantar matsala.
Guterres ya yi nuni da cewa: Miliyoyin mutane a Sudan da Zirin Gaza na cikin hadarin mutuwa ba kawai daga harsasai da bama-bamai ba, har ma da raunuka, cututtuka, da hare-haren da ba a taba ganin irinsu ba a kan cibiyoyin kiwon lafiya. Yana mai jaddada cewa: Akwai yara sama da miliyan 20 da ba sa samun allurar rigakafin yau da kullun a duniya.