Angola Ta Bukaci Tsagaita Wuta Kafin Taron Zaman Lafiya Tsakanin Kongo Demokradiyy Da Kungiyar M-23

Shugaban kasar Angolan João Lourenço, wanda kuma shi ne ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka (AU) ya yi kira ga gwamnatin Kongo

Shugaban kasar Angolan João Lourenço, wanda kuma shi ne ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka (AU) ya yi kira ga gwamnatin Kongo Democradiyya da mayakan M-23 su kawo karshen yaki kafin taron tattauna batun tsagaita wuta a gabacin kongo a ranar talata mai zuwa.

Shafin yanar gizo na labarai ‘Afirca News” ya nakalto shugaban ya na kira ga bangarorin biyu su tsagaita wuta da misalin tsakiyar daren jiya Lahadi don a tattauna batun samar da zaman lafiya cikin Nutsuwa.

Majiyar fadar shugaba shugaba Lourenco na cewa yakamata tsagaita wutar ta hada har da rashin kokarin mamayar karin iko a wasu wurare. Da kuma dakatar da fada. Har’ila yau da daina kashe fararen hula da sauransu.

An shirya taron tattaunawa ta sulhu tsakanin gwamnatin kongo Democradiyya da kuma wakilan yan tawayen M-23 zasu hadu a karon Farko don tattauna batun tsagaita budewa Juna wuta da kuma kawo karshen yaki a ranar 18 ga watan Maris, wato gobe talata , a birnin Luanda babban birnin kasar ta Angola.

Gwamnatin Kongo Democradiyya dai bata bayyana a fili kan cewa zata halarci taron sulhun wanda kasar Angola ta shirya ba, amma kungiyar M-23 ta nuna goyon bayanta ga shirin na kasar Angola. Sai dai ta yi kira ga shugaba Tsetsekedi ya bayyana anniyarsa ta zuwa taron sulhun a fili.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments