Ana Shirye-shiryen Gudanar Da Manyan Zabuka A Kasar Venezuela

A daidai lokacin da ake karatar lokacin gudanar da zaben shugaban kasr Venezuella, Shugaba Nocolas Maduro ya ce, zai amince da duk wanda hukumar zaben

A daidai lokacin da ake karatar lokacin gudanar da zaben shugaban kasr Venezuella, Shugaba Nocolas Maduro ya ce, zai amince da duk wanda hukumar zaben kasar ta sanar da cewa shi ne ya yi nasara, tare da jaddada cewa “Zaman Lafiya “ Shi ne wanda zai yi nasara.

Maduro ya kuma ce; Babu wani mahaluki da ya isa ya bata sunan kasarsa, ko kuma kawo cikas a harkar manyan zabukan da za a yi a raanr 28 ga watan nan na Yuli.

Haka nan kuma shugaban kasar ta Venezuella ya ce zai amince da duk wanda aka sanar da cewa shi ne ya lashe zaben, tare da bayyana kansa a matsayin  shugaban kasa mai cin gashin kansu, ba kuma zai zama abin wasa a hannun wani ba.

 Dangane da shirye-shiryen zabukan kasar ta Venezuela, babban mai shigar da kara na kasar Tariq Walim Sa’ab, ya ce sun aika ma’aiakata 1236 a fadin kasar da za su gudanar da zaben.

Sa’ab ya yi gargadi akan duk wani riga malam masallaci a fadin sakamakon zabe gabanin ita kanta hukumar zaben kasar,domin duk yin haka yana a karkashin laifukan zabe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments