Hukumar dake kere-kere masu alaka da sararin samaniya ta Iran ta sanar da cewa a halin yanzu tana kan ganiyar kere taurarin dan’adamguda 20 da za ake son harbawa a cikin wannan sabuwar shekarar hijira shamshiyya 1403 da aka shiga. Hukumar ta yi fatan ganin a wannan sabuwar shekarar da aka shiga an sami gagarumin cigaba ta fuskar kere-kere masu alaka da sararin samaniya,musamman tauradin dan’adama.
A shekar da ta gabata dai Iran ta yi nasarar harba taurarin dan’adam guda 7 zuwa sararin samaniya da su ka hada da’tauraron dan’adam na “Nur” na uku wanda yake cin kilo mita 7.3 a cikin kowace dakika daya.
Baya gas hi kanshi, tauraron dan’adam da Iran take kerawa, ta kuma yi nasarar kera manyan kumbo don dake harba su zuwa sararin samaniya. Na bayansu shi ne kumbo din: Kavus”.