Search
Close this search box.

Ana Ci Gaba Da Fada Tsakanin Sojojin Sudan Da Dakarun Kai Daukin Gaggawa A Omdurman

Sojojin Sudan da Dakarun kai daukin gaggawa sun yi dauki ba dadi a birnin Omdurman Rahotonni sun habarta cewa: An gwabza fada tsakanin sojojin Sudan

Sojojin Sudan da Dakarun kai daukin gaggawa sun yi dauki ba dadi a birnin Omdurman

Rahotonni sun habarta cewa: An gwabza fada tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces a yammacin birnin Omdurman. Sannan a halin da ake ciki kuma, bangarorin da suke dauke da makamai da suke kawance da sojojin Sudan a yankin Darfur sun sanar da cewa sun yi nasarar fatattakar dakarun kai daukin gaggawa daga shiyar arewacin birnin El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa.

Bangarorin da suke kawance da sojojin Sudan sun kara da cewa: Sun kwace motocin yaki guda 37 mallakin Dakarun kai daukin gaggawa tare da tarwatsa wasu motoci 23, baya ga kama wasu mayakan kungiyar Rapid Support Forces da dama da halaka wasu, sannan wasu daga cikinsu suka tsere.

A nashi bangaren, gwamnan lardin Darfur, Arko Minawi, ya bayyana fadan da ake yi tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa a birnin El Fasher, fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa, a matsayin mahimmi wajen ‘yantar da sauran yankunan na Darfur.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments