Majiyar kungiyoyin Agaji na Falasdinawa sun bayyana cewa, an fito da gawawwakin shahidai fiye da 50 daga karkashin gine-gine a garin Rafaha da Khan-Yunus dake kudancin Gaza.
Sanarwar ta kuma ce, tun bayan tsagaita wutar yaki a Gaza zuwa yanzu adadin shahidan aka fito da su daga karkashin gine-ginen da HKI ta rusa a kansu, sun kai 162.
A jiya Laraba ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu ta fitar da wani rahoto da yake cewa, jumillar shaidai da wadanda su ka jikkata a tsawonyakin da HKI ta shelanta akanal’ummar Falasdinu ya kai 47,161, yayinda wadanda su ka jikkata adadinsu ya kai 111,166.
Wata majiyar ta tabbatar da cewa baya ga wannan adadin na shaidai da akwai wani adadin da ya kai 10,000 na shahidai da suke kwance a karkashin gidajen da HKI ta rusa a kansu.