An zabi Zohran Mamdani na jam’iyyar Democrat a matsayin Magajin Garin New York, inda ya kayar da Curtis Sliwa na Republican da Andrew Cuomo dan Takara mai zaman kansa, sannan ya kafa tarihi a matsayin Musulmi na farko kuma magajin gari mafi karancin shekaru a birnin cikin sama da shekaru 100.
Mamdani, mai shekaru 34, ya samu kashi 50.4% na dukkanin kuri’un da aka kada, yayin da Sliwa ya samu kashi 41.3%, a cewar sakamakon Hukumar Zabe, Ana sa ran zai fara aiki a ranar 1 ga Janairu 2026.
A halin yanzu yana aiki a Majalisar Dokokin Jihar New York, Mamdani yana da alaĆ™a da Jam’iyyar Democrat Socialist kuma ya kasance mai sukar manufofin Shugaba Donald Trump. Nasarar da ya samu, wacce matasa suka taka muhimmiyar rawa wajen nuna masa goyon baya, ana ganin ta kawo wani gagarumin sauyi a shugabancin birni mai muhimmanci a Amurka.
Kafofin yada labarai irin su Associated Press, CNN, da Bloomberg sun bayar da rahotanni da ke nuni da cewa yawan masu kada kuri’a ya zarce miliyan 2, wanda shi ne mafi girma na masu kada kuri’a da aka gani a fagen siyasar NYC.
Nasarar Mamdani ta zo ne tare da nasarorin jam’iyyar Democrat a jihohin Virginia da New Jersey, inda jam’iyyar ta ci gaba da rike kujerun gwamnoni, wanda hakan ya kara tabbatar da nasarar jam’iyyar Democrat a manyan jihohi kafin zaben 2026.