Shugaban kungiyar agajin Falasdinawa ta “UNRWA’ wacce MDD ta kafa, ya yi gargadin rushewarta da hakan zai hana Falasdinawa na yanzu samun ilimi, haka nan kuma bayar da kayan agaji da bukatun yau da kullum ga mutane miliyan 6 a Falasdinu.
Shugaban kungiyar Agajin Philippe Lazzarini ya fada wa kamfanin dillancin labarun Faransa cewa; Da akwai hatsari da gaske da kungiyar take fuskanta na rushewa, da hakan zai kara dagula yanayin da al’ummar Falasdinu suke ciki.”
Philippe Lazzarini ya kara da cewa; Idan hakan ta faru, to mun sadaukar da falasdinawan da suke rayuwa a wannan lokacin da hana su ilimi.
Tun bayan farmakon Aksa 2023 ne dai HKI da Amurka su ka dauki matakin haramta kungiyar da dakatar da duk wani aiki da ita.
MDD ce dai ta kafa wannan kungiyar domin taimakawa Falasdinawan da kirkirar HKI ya yi sanadiyyar mayar da su ‘yan gudun hijira.
Wasu kasashe da kuma kungiyoyi da dama a duniya sun yi tir da matakin na HKI da kuma Amurka akan wannan kungiya.
Da akwai yaran Falasdinawa 100,000 a cikin Gada kadai da suke karatu a karkashin makarantun kungiyar.
Philippe Lazzarini ya ce, idan aka hana wadannan yaran karatu to mun shuka irin tsattsauran ra’ayi, wanda zai zama babban bala’i.