An Yi Bikin Cika Shekaru 46 Na Nasarar Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran, A Burkina Faso

Iraniyawa mazauna kasar Burkina Faso sun gudanar da bukukuwan murnar cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a birnin Ouagadougou. A wannan

Iraniyawa mazauna kasar Burkina Faso sun gudanar da bukukuwan murnar cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a birnin Ouagadougou.

A wannan karon, kasashen biyu sun daukaka kyakkyawar dangantakarsu da aka gina a shekarar 1984.  

Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Ouagadougou, Mojtaba Faghihi, wanda ya halarci bikin, ya bayyana cewa juyin juya halin Musulunci a Iran a shekara ta 1979 ya ba da damar “yantar da mu daga tsoma bakin siyasa na kasashen waje da wawashe dukiyarmu”.

A cewarsa, Iran ta samu nasarar dakile makircin makiya da kuma wuce gona da iri na sojojin kasashen waje, da takunkumi da kuma ta’addanci.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Burkina Faso, Karamoko Jean-Marie Traoré, ya bayyana jin dadinsa da raba wannan lokaci karkashin alamar abota da hadin kai tsakanin al’ummomin kasashen biyu, wadanda suka yanke shawarar tafiya tare tun daga shekarar 1984.

Ya kuma mika sakon shugaban Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traoré, na taya murna dangane da cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci.

A cewarsa, Iran ita ma kasa ce “da za mu iya koyo daga gare ta, musamman daga juriyarta, hazaka da jaruntaka”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments