An Tsawaita Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsakanin Isra’ila Da Lebanon Har Zuwa 18 Ga Watan Fabrairu

An tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon na tsawon kimanin makonni uku bayan da gwamnatin kasar ta ki janye dakarunta kamar yadda

An tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon na tsawon kimanin makonni uku bayan da gwamnatin kasar ta ki janye dakarunta kamar yadda aka kulla da farko.

An bayyana cewa yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025.

Shi ma firaministan kasar Labanon Najib Mikati ya tabbatar da tsawaita wa’adin, yana mai kara da cewa Lebanon za ta mutunta hakan.

Bisa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka sanar tsakanin Isra’ila da Hizbullah a watan Nuwamba, a jiya ne ya kamata sojojin Isra’ila su fice daga kudancin Lebanon.

“Gwamnatin Lebanon ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025,” in ji Mikati a cikin wata sanarwa, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

Duk da haka a ranar Lahadi sojojin Isra’ila sun bude wuta kan al’ummar Lebanon da ke kokarin komawa gidajensu a kudancin kasar, inda suka kashe fararen hula akalla 22 tare da jikkata wasu fiye da 120 na daban.

‘Yan kasar ta Lebanon, sun sha alwashin komawa kauyuka da garuruwansu, duk da barazanar da Isra’ila ke yi.

A karshen mako ne, sojojin Isra’ila suka gargadi al’ummar Lebanon da kada su koma garuruwansu na kudancin kasar.

Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hizbullah a ranar 27 ga watan Nuwamban 2024, bayan ta tafka asara mai yawa a fagen daga da kuma kasa cimma burinta duk da kashe mutane sama da 4,000 a Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments