Kafafen yada labarai na HKI sun tabbatar da mutuwar wasu da dama daga cikin sojojin su a wani tarkon da dakarun Hamas suka yi masau a garin Khan Yunus na Gaza, wasu sun ji nrauni, sannan har yanzun akwai wadanda ba’a fito dasu daga karkashin burbushin gine-gine ba.
Kamfanin dillancin labatan IP na kasar Iran. Majiyar yahudawan ta kara da cewa karfin da kungiyar Hamas ta tokwarorinsu suke da shin a halaka sojojin HKI kamar haka ya Sanya shakku a kan yiyuwar samun nasara a kansu.
Kamfanin dillancin labaran Hadashot Bazman na yahudawan ya tabbatar da cewa an kashe yahudawa 5 sannan wasu 12 sun ji Rauni a yayinda har yanzun ba’a san halin da wasu daga cikin sojojin suke ciki a karkashin kasa ba.
Rahoton ba bayyana cewa an ga jirage masu saukar ungulu suna kai kawo daga asbiti zuwa inda abin ya faru a Khan Yunus.