Search
Close this search box.

An Kashe Sojojin HKI 3  A Kusa Da Garin Hebron na Yankin Yamma Da Kogin Jordan

Akalla sojojin HKI biyu ne suka halaka, sannan wani bayahude dan share wuri zauna guda shi ma ya halaka a wani harin da dakarun Falasdinawa

Akalla sojojin HKI biyu ne suka halaka, sannan wani bayahude dan share wuri zauna guda shi ma ya halaka a wani harin da dakarun Falasdinawa suka kai masu a kusa da garin Hebron na yankin yamma da kogin Jordan.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wata tashar radiyo ta HKI na fadar cewa an kashe bayahuwan uku ne a garin Tarqumiyah kusa da garin Hebron . Labaran da tashar radiyo ta sojojin HKI ta bayar ya nuna cewa mutum na uku wanda aka kashe dan shekara kimani 50 a duniya ne.

Radiyon yahudawan ta bayyana cewa a halin yanzo jami’an tsaron kasar suna neman wadanda suka yi kissan a cikin Falasdinawa a garin Khalil da wasu wurare.

Kafin haka dai tashar radiyon ta bada labarin mutuwar mutane biyu yan shekaru kimani 30-30 a kusa da garin Hebron dake yankin yamma da kogin Jordan.

Har’ila yau majiyar yahudawan ta bayyana a shafin X kan cewa sun fara bincike don neman wadanda suka yi kissan. Kuma zasu samesu nan kusa. Sannan ta kammala da cewa mutane biyu na farko da aka kashe dai yansandan HKI ne wadanda suke aiki a kan iyakokin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments