Dubban daruruwan mutanen kasar Yemen ne suka fito a birnin San’aa babban birnin kasar ta kuma sauran yankuna a jiya Jumma’a don nuna goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu musamman gaza, bisa yakin da suke fafatawa da HKI fiye da watanni 14 da suka gabata.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa suna tare da mutanen Gaza duk tare da hare-haren da HKI take kaiwa kan kasar. Sun ce ba zasu taba jada baya ba. Sun kuma kara da cewa goyon bayan falasdinu wajibine na addini a wajensu.
A wani labarin kuma sojojin kasar ta Yemen sun cilla makamai masu linzami samfurin bilistic wanda ya fada kan Yafa, ko tel-aviv, a jiya Jumma’a. Sannan tashar talabijin ta 12 ta HKI ta bada labarin jikkadan yahudawa akalla 18.
Banda haka dubban mutane sun yi ta gudu zuwa wuraren buya, bayan sun ji jiniyar gargadi na tashi a birnin.
Kasar Yemen dai tana taimakawa Falasdinwa ta hanyar hana jiragen ruwa zuwa tashoshin jiragen ruwa na HKI da kuma cilla makamai masu linzami kanta.