An Guadanar Da Janazar Manyan Jami’an Gwamnatin Yemen Da Suka Yi Shahada A Harin Isra’ila

An gudanar da janazar manyan jami’an gwamnatin kasar Yemen 9 da suka yi shahada a wani harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kaddamar a kansu,a 

An gudanar da janazar manyan jami’an gwamnatin kasar Yemen 9 da suka yi shahada a wani harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kaddamar a kansu,a  lokacin da suke gudanar da wani zama na gwamnati, domin bin kadun ayyukan ma’aikatun da suke jagoranta.

Dubban daruruwan mutane ne dai suka halarci janazar wadda ta gudana a birnin San’a fadar mulkin kasar ta Yemen a jiya, inda aka gabatar da jawabai daban-daban, da ke kara tabbatar da aniyar al’ummar kasar Yemen wajen ci gaba da bin tafarkin wadanda suka yi shahada, domin mara baya ga al’ummar Gaza mara kariya.

A nasa bangaren Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul Malik al-Houthi ya yi kakkausar suka kan wannan hari na wuce gona da iri da Isra’ila ta kai a birnin San’a, wanda ya kai ga shahadar wadannan manyan jami’ai  da suka hada har da firaministan kasar ta Yemen da wasu ministoci.

A cikin  jawabin da ya yi ta gidan talabijin, al-Houthi ya bayyana cewa, “laifi ne kai hari kan ministoci da ma’aikata farar hula ya kara tabbatar da laifukan Haramtacciyar Kasar Isra’ila a yankin,” yana mai jaddada cewa dukkan wadanda suka yi shahada suna gudanar da ayyukansu ne a fagagen da ba na soja ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments