An gado gawar Marine Vlahovic wata yar jarida da ta shahara a goyon bayan Falasdinawa a garin Marseille na kasar Faransa, kuma an kasheta ne a lokacinda take cikin shirya wani shiri numusamman wanda ya tattara bayanai dangane da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza, da kuma gwagwarmayan Falasdinawa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce Vlohovic diyar shekara 39 a duniya ta shahara da goyon bayan falasdinawa kuma ta gabatar da shirye-shiryen Sau da dama don nuna irin kissan kare dangin sojojin yahudawa suke yi a Gaza.
A ranar 25 ga watan Nuwamban da ya gabata ne wasu abokanta Vlohovic suka fahinci cewa bata daukart waya kuma bata amsa sakonni, sai suka je gidanta inda suka sami cewa ta mutu. Tuni dai gwamnatin kasar faransa ta fara bincike don gano abinda ya faru da ita.
Vlohovic dai ta yi aiki da mashahuran kafafen yada labarai na kasar faransa, wadanda suka hada da RTS, Le Soir, RFI, Radio Faransa da kuma Libération.