An Fara Gudanar Da Zaman Taron Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Tsakanin Iran Da Kasashen Nahiyar Afirka

An fara gudanar da zaman taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin  Iran da kasashen nahiyar Afirka karo na uku A safiyar yau Lahadi ne aka

An fara gudanar da zaman taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin  Iran da kasashen nahiyar Afirka karo na uku

A safiyar yau Lahadi ne aka bude zaman taron karo na uku kan harkokin tattalin arziki tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen Afirka a birnin Tehran, tare da halartar shugaban kasar Iran da mataimakinsa na farko da wasu tawagar jami’ai da ‘yan kasuwa daga nahiyar Afirka.

Kasar Iran tana gudanar da wannan biki ne tare da jami’an kungiyar Tarayyar Afirka, da manyan jami’ai, ministocin tattalin arziki da cinikayya, da shugabannin kungiyoyin kasuwanci, ‘yan kasuwa, masu fafutukar tattalin arziki, shugabannin bankuna, kamfanonin inshora, da na’urorin samar da kayayyaki, da daraktocin manyan kamfanoni da na kasa da kasa daga kasashen Afirka.

Taron hadin gwiwar tattalin arziki na Iran da Afirka na wakiltar wani sauyi a tsarin Iran na samar da hadin gwiwa da kasashen nahiyar ta Afirka. A Juyin lokaci a cikin hanyoyin haɗin gwiwa, nahiyar Afirka tana wakiltar wata dama ta musamman ga kasashe masu tasowa ta hanyar kasuwanci. Kasashen Afirka na bukatar su shigo da kayayyaki, da ayyuka, da kwararrun ma’aikata domin shawo kan koma bayan da suka fuskanta a tarihi, kuma Iran da alama tana iyaka kokarinta na taimakawa kasashen Afirka a wannan fanni.

A ranar Litinin ne ‘yan kasuwar za su ziyarci baje kolin Iran, kuma a ranar Talata bayan kammala wani taron karawa juna sani a zauren taron koli na tekun Fasha, za su nufi birnin Isfahan, tare da rakiyar tawagogin gwamnati da ‘yan kasuwar Afirka, inda za su gudanar da taruka na musamman da kuma ziyartar cibiyoyi da masana’antu fiye da 10 a lardin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments