Kamfanin dillancin labarun “Isna” ya nakalto majiyar shari’a ta kasar Faransa tana cewa an dauke wata bafaranshiya mai suna Amira Zaita shekaru uku a gidan kurkuku saboda rajin goyon bayan Falasdinawa ta hanyar kafafen sadarwa na al’umma.
Wata kotun da take a garin “Nice” na kasar Faransa ce ta yanke hukuncin zaman kurkukun ga matar ‘yar shekaru 34, wacce daliba ne a makarantar koyon jiyya a shekarar karatu ta biyu.
Matar tana cikin wadanda su ka kafa wata kungiyar da aka bai wa sunan: “Daga Nice Zuwa Gaza” , kuma a duk lokacin da ake yin jerin gwanon nuna goyon bayan Falasdinawa tana ciki.
A lokacin da ake yi mata sharia, ta fadawa kotu cewa; Abinda yake faruwa a Gaza, kisan kiyashi ne da ya zuwa yanzu an kashe mutane fiye da 43,000 kuma an jikkata wasu da sun haura 100,000.
Baya ga yanke mata hukuncin zaman kurkuku na shekaru 3 an kuma ci tararta na kudin da su ka kai yuro 13,500.